Za'a ce da ma'abocin Alkur’ani: Karanta ka daukaka, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya, domin cewa matsayinka zai tasayane a karshen ayar da ka karantata

Scan the qr code to link to this page

Hadith
Bayani
Manufofin Fassarorin
Daga Cikin Fa idodin Hadisin
kashe kashe
Kari
Daga Abdullahi dan Amr dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Za'a ce da ma'abocin Alkur’ani: Karanta ka daukaka, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya, domin cewa matsayinka zai tasayane a karshen ayar da ka karantata".
Hasan ne - Abu Daud Ya Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa, za’a ce da makarancin Alkur’ani, mai aiki da abinda ke cikinsa, wanda ya lazimceshi a karatu da hadda idan ya shiga Aljanna: Ka karanta ka daukaka da wannan a cikin darajojin Aljanna, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya da karanta shi da bi ahankali da nutsuwa; domin cewa matsayinka na karshen ayar da ka karantata ne.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Sakayya tana daidai da dacewar ayyuka a yawa da yanayi.
  2. Kwadaitarwa akan karatun Alkur’ani da kyautata shi da hardace shi da tadabburi da kuma aiki da shi.
  3. Aljanna masaukaice darajoji masu yawa, ma'abota Alkur’ani zasu samu madaukakan darajoji a cikinta.

kashe kashe

An aika shi cikin Nasara