Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana karkasuwar mutane a karatun AlKur'ani da amfanuwa da shi:
Kashi na farko: Muminin da yake karanta AlKur'ani kuma yake amfanuwa da shi, to shi kamar gawasa ne, mai dadin dandano da kanshi, da kyakkyawan launi, kuma amfaninsa mai yawa ne, shi yana aiki da abinda ya karanta, kuma yana amfanar bayin Allah.
Kashi na biyu: Muminin da ba ya karanta AlKur'ani, to shi kamar dabino ne, dandanonsa mai zaki ne, kuma ba shi da kanshi, to zuciyarsa mai tattare da imani ce kamar tattarowar dabino akan zaki a dandanonsa da cikinsa, da rashin bayyanar kanshi gare shi wanda mutane za su shaka; Saboda rashin bayyanar karatu daga gare shi wanda mutane za su ji dadin jinsa.
Na uku: Munafikin da yake karanta AlKur'ani: To shi kamar nana ne, tana da dadin kanshi kuma dandanonta mai daci ne, ta inda bai gyara zuciyarsa da imani ba, kuma bai yi aiki da AlKur'ani ba, kuma yana bayyana ga mutane cewa shi muminine, to kanshinta mai dadi yana kama da karatunsa, dandanonta mai daci kuma yana kama da kafircinsa.
Na hudu: Munafikin da ba ya karanta AlKur'ani, to shi kamar guna ne, ta inda ita ba ta da kanshi, da kuma dacin dandanonta, to rashin kanshinta ya yi kama da rashin kanshinsa; Saboda rashin karatunsa, kuma dacin dandanonta ya yi kama da dacin kafircinsa, cikinsa ya kadaita daga imani, zahirinsa kuma babu amfani a cikinsa, kai shi mai cutarwa ne.