Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya sanin rabewar sura har sai {Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai} ta sauka a gare shi

Scan the qr code to link to this page

Hadith
Bayani
Manufofin Fassarorin
Daga Cikin Fa idodin Hadisin
kashe kashe
Kari
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya sanin rabewar sura har sai {Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai} ta sauka a gare shi.
Ingantacce ne - Abu Daud Ya Rawaito shi

Bayani

Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - yana bayyana cewa surorin Alkur’ani sun kasance suna sauka ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - amma ba ya sanin rabewarsu da karewarsu har sai {Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai} ta sauka gareshi, sai ya san cewa surar da ta gabata an cikata, kuma cewa ita farko ce ga sabuwar sura.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Baslamalah ana rabewa da ita tsakanin surori, saidai tsakanin Suratul Anfal da Suratul Taubah.

kashe kashe

An aika shi cikin Nasara